Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 100 a Alƙur'ani

Sura Al-'Adiyat

Makkiyya Aya 11 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلْعَٰدِيَٰتِ ضَبْحًۭا ﴿١﴾

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

فَٱلْمُورِيَٰتِ قَدْحًۭا ﴿٢﴾

Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

فَٱلْمُغِيرَٰتِ صُبْحًۭا ﴿٣﴾

Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

فَأَثَرْنَ بِهِۦ نَقْعًۭا ﴿٤﴾

Sai su motsar da ƙũra game da shi.

فَوَسَطْنَ بِهِۦ جَمْعًا ﴿٥﴾

Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.

إِنَّ ٱلْإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٌۭ ﴿٦﴾

Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌۭ ﴿٧﴾

Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.

وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلْخَيْرِ لَشَدِيدٌ ﴿٨﴾

Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِى ٱلْقُبُورِ ﴿٩﴾

Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

وَحُصِّلَ مَا فِى ٱلصُّدُورِ ﴿١٠﴾

Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍۢ لَّخَبِيرٌۢ ﴿١١﴾

Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Al-'Adiyat Aya 1 cikin 11

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-'Adiyat

Sura Al-'Adiyat (العاديات) ita ce sura ta 100 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 11 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, العاديات, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-'Adiyat

Ayoyi nawa ne a Sura Al-'Adiyat?

Sura Al-'Adiyat tana da ayoyi 11.

Shin Sura Al-'Adiyat ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-'Adiyat take?

Sura Al-'Adiyat tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-'Adiyat?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp