ٱلْقَارِعَةُ ﴿١﴾
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
Sura ta 101 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلْقَارِعَةُ ﴿١﴾
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
مَا ٱلْقَارِعَةُ ﴿٢﴾
Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْقَارِعَةُ ﴿٣﴾
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
يَوْمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلْفَرَاشِ ٱلْمَبْثُوثِ ﴿٤﴾
Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
وَتَكُونُ ٱلْجِبَالُ كَٱلْعِهْنِ ٱلْمَنفُوشِ ﴿٥﴾
Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَٰزِينُهُۥ ﴿٦﴾
To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
فَهُوَ فِى عِيشَةٍۢ رَّاضِيَةٍۢ ﴿٧﴾
To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَٰزِينُهُۥ ﴿٨﴾
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٌۭ ﴿٩﴾
To, uwarsa Hãwiya ce.
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا هِيَهْ ﴿١٠﴾
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
نَارٌ حَامِيَةٌۢ ﴿١١﴾
Wata wuta ce mai zafi.
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura Al-Qari'ah (القارعة) ita ce sura ta 101 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 11 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, القارعة, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura Al-Qari'ah tana da ayoyi 11.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura Al-Qari'ah tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.