Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 102 a Alƙur'ani

Sura At-Takathur

Makkiyya Aya 8 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

أَلْهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ ﴿١﴾

Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).

حَتَّىٰ زُرْتُمُ ٱلْمَقَابِرَ ﴿٢﴾

Har kuka ziyarci kaburbura.

كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ ﴿٣﴾

A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.

ثُمَّ كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ ﴿٤﴾

Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.

كَلَّا لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ ٱلْيَقِينِ ﴿٥﴾

Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.

لَتَرَوُنَّ ٱلْجَحِيمَ ﴿٦﴾

Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.

ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ ٱلْيَقِينِ ﴿٧﴾

Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.

ثُمَّ لَتُسْـَٔلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ ﴿٨﴾

Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).

At-Takathur Aya 1 cikin 8

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura At-Takathur

Sura At-Takathur (التكاثر) ita ce sura ta 102 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 8 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, التكاثر, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura At-Takathur

Ayoyi nawa ne a Sura At-Takathur?

Sura At-Takathur tana da ayoyi 8.

Shin Sura At-Takathur ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura At-Takathur take?

Sura At-Takathur tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura At-Takathur?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp