Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 91 a Alƙur'ani

Sura Ash-Shams

Makkiyya Aya 15 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلشَّمْسِ وَضُحَىٰهَا ﴿١﴾

Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.

وَٱلْقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا ﴿٢﴾

Kuma da wata idan ya bi ta.

وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا ﴿٣﴾

Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.

وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰهَا ﴿٤﴾

Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا ﴿٥﴾

Da sama da abin da ya gina ta.

وَٱلْأَرْضِ وَمَا طَحَىٰهَا ﴿٦﴾

Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

وَنَفْسٍۢ وَمَا سَوَّىٰهَا ﴿٧﴾

Da rai da abin da ya daidaita shi.

فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَىٰهَا ﴿٨﴾

Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.

قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّىٰهَا ﴿٩﴾

Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.

وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا ﴿١٠﴾

Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.

كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَىٰهَآ ﴿١١﴾

Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشْقَىٰهَا ﴿١٢﴾

A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقْيَٰهَا ﴿١٣﴾

Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمْ فَسَوَّىٰهَا ﴿١٤﴾

Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

وَلَا يَخَافُ عُقْبَٰهَا ﴿١٥﴾

Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

Ash-Shams Aya 1 cikin 15

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Ash-Shams

Sura Ash-Shams (الشمس) ita ce sura ta 91 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 15 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, الشمس, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Ash-Shams

Ayoyi nawa ne a Sura Ash-Shams?

Sura Ash-Shams tana da ayoyi 15.

Shin Sura Ash-Shams ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Ash-Shams take?

Sura Ash-Shams tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Ash-Shams?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp