Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 92 a Alƙur'ani

Sura Al-Layl

Makkiyya Aya 21 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰ ﴿١﴾

Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.

وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ ﴿٢﴾

Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.

وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ ﴿٣﴾

Da abin da ya halitta namiji da mace.

إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰ ﴿٤﴾

Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.

فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَٱتَّقَىٰ ﴿٥﴾

To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.

وَصَدَّقَ بِٱلْحُسْنَىٰ ﴿٦﴾

Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.

فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْيُسْرَىٰ ﴿٧﴾

To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.

وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسْتَغْنَىٰ ﴿٨﴾

Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.

وَكَذَّبَ بِٱلْحُسْنَىٰ ﴿٩﴾

Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.

فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْعُسْرَىٰ ﴿١٠﴾

To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.

وَمَا يُغْنِى عَنْهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ ﴿١١﴾

Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).

إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰ ﴿١٢﴾

Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.

وَإِنَّ لَنَا لَلْءَاخِرَةَ وَٱلْأُولَىٰ ﴿١٣﴾

Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.

فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًۭا تَلَظَّىٰ ﴿١٤﴾

Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.

لَا يَصْلَىٰهَآ إِلَّا ٱلْأَشْقَى ﴿١٥﴾

Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.

ٱلَّذِى كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ﴿١٦﴾

Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.

وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلْأَتْقَى ﴿١٧﴾

Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.

ٱلَّذِى يُؤْتِى مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ ﴿١٨﴾

Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.

وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعْمَةٍۢ تُجْزَىٰٓ ﴿١٩﴾

Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.

إِلَّا ٱبْتِغَآءَ وَجْهِ رَبِّهِ ٱلْأَعْلَىٰ ﴿٢٠﴾

Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.

وَلَسَوْفَ يَرْضَىٰ ﴿٢١﴾

To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).

Al-Layl Aya 1 cikin 21

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-Layl

Sura Al-Layl (الليل) ita ce sura ta 92 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 21 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, الليل, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Layl

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Layl?

Sura Al-Layl tana da ayoyi 21.

Shin Sura Al-Layl ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Layl take?

Sura Al-Layl tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-Layl?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp