وَٱلضُّحَىٰ ﴿١﴾
Inã rantsuwa da hantsi.
Sura ta 93 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلضُّحَىٰ ﴿١﴾
Inã rantsuwa da hantsi.
وَٱلَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ ﴿٢﴾
Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ ﴿٣﴾
Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
وَلَلْءَاخِرَةُ خَيْرٌۭ لَّكَ مِنَ ٱلْأُولَىٰ ﴿٤﴾
Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰٓ ﴿٥﴾
Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًۭا فَـَٔاوَىٰ ﴿٦﴾
Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
وَوَجَدَكَ ضَآلًّۭا فَهَدَىٰ ﴿٧﴾
Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
وَوَجَدَكَ عَآئِلًۭا فَأَغْنَىٰ ﴿٨﴾
Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
فَأَمَّا ٱلْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ ﴿٩﴾
Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنْهَرْ ﴿١٠﴾
Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ ﴿١١﴾
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura Ad-Duha (الضحى) ita ce sura ta 93 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 11 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, الضحى, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura Ad-Duha tana da ayoyi 11.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura Ad-Duha tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.