وَيْلٌۭ لِّكُلِّ هُمَزَةٍۢ لُّمَزَةٍ ﴿١﴾
Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
Sura ta 104 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَيْلٌۭ لِّكُلِّ هُمَزَةٍۢ لُّمَزَةٍ ﴿١﴾
Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
ٱلَّذِى جَمَعَ مَالًۭا وَعَدَّدَهُۥ ﴿٢﴾
Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخْلَدَهُۥ ﴿٣﴾
Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
كَلَّا ۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِى ٱلْحُطَمَةِ ﴿٤﴾
A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْحُطَمَةُ ﴿٥﴾
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
نَارُ ٱللَّهِ ٱلْمُوقَدَةُ ﴿٦﴾
Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
ٱلَّتِى تَطَّلِعُ عَلَى ٱلْأَفْـِٔدَةِ ﴿٧﴾
Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
إِنَّهَا عَلَيْهِم مُّؤْصَدَةٌۭ ﴿٨﴾
Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
فِى عَمَدٍۢ مُّمَدَّدَةٍۭ ﴿٩﴾
A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura Al-Humazah (الهمزة) ita ce sura ta 104 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 9 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, الهمزة, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura Al-Humazah tana da ayoyi 9.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura Al-Humazah tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.