هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْغَٰشِيَةِ ﴿١﴾
Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
Sura ta 88 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْغَٰشِيَةِ ﴿١﴾
Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
وُجُوهٌۭ يَوْمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ ﴿٢﴾
Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
عَامِلَةٌۭ نَّاصِبَةٌۭ ﴿٣﴾
Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
تَصْلَىٰ نَارًا حَامِيَةًۭ ﴿٤﴾
Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
تُسْقَىٰ مِنْ عَيْنٍ ءَانِيَةٍۢ ﴿٥﴾
Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍۢ ﴿٦﴾
Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
لَّا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِى مِن جُوعٍۢ ﴿٧﴾
Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
وُجُوهٌۭ يَوْمَئِذٍۢ نَّاعِمَةٌۭ ﴿٨﴾
Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
لِّسَعْيِهَا رَاضِيَةٌۭ ﴿٩﴾
Game da aikinsu, masu yarda ne.
فِى جَنَّةٍ عَالِيَةٍۢ ﴿١٠﴾
(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةًۭ ﴿١١﴾
Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
فِيهَا عَيْنٌۭ جَارِيَةٌۭ ﴿١٢﴾
A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
فِيهَا سُرُرٌۭ مَّرْفُوعَةٌۭ ﴿١٣﴾
A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
وَأَكْوَابٌۭ مَّوْضُوعَةٌۭ ﴿١٤﴾
Da kõfuna ar'aje.
وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌۭ ﴿١٥﴾
Da filõli jẽre,
وَزَرَابِىُّ مَبْثُوثَةٌ ﴿١٦﴾
Da katifu shimfiɗe.
أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ ﴿١٧﴾
Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيْفَ رُفِعَتْ ﴿١٨﴾
Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
وَإِلَى ٱلْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ ﴿١٩﴾
Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
وَإِلَى ٱلْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ ﴿٢٠﴾
Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
فَذَكِّرْ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٌۭ ﴿٢١﴾
sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ ﴿٢٢﴾
Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ ﴿٢٣﴾
Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَكْبَرَ ﴿٢٤﴾
To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
إِنَّ إِلَيْنَآ إِيَابَهُمْ ﴿٢٥﴾
Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُم ﴿٢٦﴾
Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura Al-Ghashiyah (الغاشية) ita ce sura ta 88 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 26 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, الغاشية, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura Al-Ghashiyah tana da ayoyi 26.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura Al-Ghashiyah tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.