سَبِّحِ ٱسْمَ رَبِّكَ ٱلْأَعْلَى ﴿١﴾
Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
Sura ta 87 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
سَبِّحِ ٱسْمَ رَبِّكَ ٱلْأَعْلَى ﴿١﴾
Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
ٱلَّذِى خَلَقَ فَسَوَّىٰ ﴿٢﴾
Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
وَٱلَّذِى قَدَّرَ فَهَدَىٰ ﴿٣﴾
Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
وَٱلَّذِىٓ أَخْرَجَ ٱلْمَرْعَىٰ ﴿٤﴾
Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحْوَىٰ ﴿٥﴾
Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ ﴿٦﴾
Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُ ۚ إِنَّهُۥ يَعْلَمُ ٱلْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ ﴿٧﴾
Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ ﴿٨﴾
Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكْرَىٰ ﴿٩﴾
Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰ ﴿١٠﴾
Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلْأَشْقَى ﴿١١﴾
Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
ٱلَّذِى يَصْلَى ٱلنَّارَ ٱلْكُبْرَىٰ ﴿١٢﴾
Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ ﴿١٣﴾
Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰ ﴿١٤﴾
Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
وَذَكَرَ ٱسْمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ ﴿١٥﴾
Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
بَلْ تُؤْثِرُونَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا ﴿١٦﴾
Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
وَٱلْءَاخِرَةُ خَيْرٌۭ وَأَبْقَىٰٓ ﴿١٧﴾
Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
إِنَّ هَٰذَا لَفِى ٱلصُّحُفِ ٱلْأُولَىٰ ﴿١٨﴾
Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
صُحُفِ إِبْرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ ﴿١٩﴾
Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura Al-A'la (الأعلى) ita ce sura ta 87 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 19 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, الأعلى, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura Al-A'la tana da ayoyi 19.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura Al-A'la tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.