وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ ﴿١﴾
Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
Sura ta 86 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ ﴿١﴾
Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ ﴿٢﴾
To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
ٱلنَّجْمُ ٱلثَّاقِبُ ﴿٣﴾
Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.
إِن كُلُّ نَفْسٍۢ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌۭ ﴿٤﴾
Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
فَلْيَنظُرِ ٱلْإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ ﴿٥﴾
To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
خُلِقَ مِن مَّآءٍۢ دَافِقٍۢ ﴿٦﴾
An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
يَخْرُجُ مِنۢ بَيْنِ ٱلصُّلْبِ وَٱلتَّرَآئِبِ ﴿٧﴾
Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجْعِهِۦ لَقَادِرٌۭ ﴿٨﴾
Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
يَوْمَ تُبْلَى ٱلسَّرَآئِرُ ﴿٩﴾
Rãnar da ake jarrabawar asirai.
فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٍۢ وَلَا نَاصِرٍۢ ﴿١٠﴾
Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجْعِ ﴿١١﴾
Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
وَٱلْأَرْضِ ذَاتِ ٱلصَّدْعِ ﴿١٢﴾
Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
إِنَّهُۥ لَقَوْلٌۭ فَصْلٌۭ ﴿١٣﴾
Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
وَمَا هُوَ بِٱلْهَزْلِ ﴿١٤﴾
Kuma shĩ bã bananci bane
إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًۭا ﴿١٥﴾
Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
وَأَكِيدُ كَيْدًۭا ﴿١٦﴾
Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
فَمَهِّلِ ٱلْكَٰفِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًۢا ﴿١٧﴾
Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura At-Tariq (الطارق) ita ce sura ta 86 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 17 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, الطارق, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura At-Tariq tana da ayoyi 17.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura At-Tariq tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.