Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 85 a Alƙur'ani

Sura Al-Buruj

Makkiyya Aya 22 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلْبُرُوجِ ﴿١﴾

Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.

وَٱلْيَوْمِ ٱلْمَوْعُودِ ﴿٢﴾

Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,

وَشَاهِدٍۢ وَمَشْهُودٍۢ ﴿٣﴾

Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa

قُتِلَ أَصْحَٰبُ ٱلْأُخْدُودِ ﴿٤﴾

An la'ani mutãnen rãmi.

ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلْوَقُودِ ﴿٥﴾

Wato wuta wadda aka hura.

إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌۭ ﴿٦﴾

A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.

وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِٱلْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌۭ ﴿٧﴾

Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.

وَمَا نَقَمُوا۟ مِنْهُمْ إِلَّآ أَن يُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَمِيدِ ﴿٨﴾

Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.

ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍۢ شَهِيدٌ ﴿٩﴾

Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.

إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُوا۟ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَٰتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا۟ فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ ٱلْحَرِيقِ ﴿١٠﴾

Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمْ جَنَّٰتٌۭ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَٰرُ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْكَبِيرُ ﴿١١﴾

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.

إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ ﴿١٢﴾

Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.

إِنَّهُۥ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ ﴿١٣﴾

Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).

وَهُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلْوَدُودُ ﴿١٤﴾

Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.

ذُو ٱلْعَرْشِ ٱلْمَجِيدُ ﴿١٥﴾

Mai Al'arshi mai girma

فَعَّالٌۭ لِّمَا يُرِيدُ ﴿١٦﴾

Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.

هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْجُنُودِ ﴿١٧﴾

Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.

فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ ﴿١٨﴾

Fir'auna da samũdãwa?

بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فِى تَكْذِيبٍۢ ﴿١٩﴾

Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.

وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطٌۢ ﴿٢٠﴾

Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).

بَلْ هُوَ قُرْءَانٌۭ مَّجِيدٌۭ ﴿٢١﴾

Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.

فِى لَوْحٍۢ مَّحْفُوظٍۭ ﴿٢٢﴾

A cikin Allo tsararre.

Al-Buruj Aya 1 cikin 22

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-Buruj

Sura Al-Buruj (البروج) ita ce sura ta 85 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 22 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, البروج, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Buruj

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Buruj?

Sura Al-Buruj tana da ayoyi 22.

Shin Sura Al-Buruj ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Buruj take?

Sura Al-Buruj tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-Buruj?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp