Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 84 a Alƙur'ani

Sura Al-Inshiqaq

Makkiyya Aya 25 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتْ ﴿١﴾

Idan sama ta kẽce,

وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ ﴿٢﴾

Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,

وَإِذَا ٱلْأَرْضُ مُدَّتْ ﴿٣﴾

Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,

وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ ﴿٤﴾

Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.

وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ ﴿٥﴾

Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,

يَٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدْحًۭا فَمُلَٰقِيهِ ﴿٦﴾

Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.

فَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ ﴿٧﴾

To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.

فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًۭا يَسِيرًۭا ﴿٨﴾

To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.

وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًۭا ﴿٩﴾

Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.

وَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهْرِهِۦ ﴿١٠﴾

Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.

فَسَوْفَ يَدْعُوا۟ ثُبُورًۭا ﴿١١﴾

To, zã shi dinga kiran halaka!

وَيَصْلَىٰ سَعِيرًا ﴿١٢﴾

Kuma ya shiga sa'ĩr.

إِنَّهُۥ كَانَ فِىٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًا ﴿١٣﴾

Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.

إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ ﴿١٤﴾

Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.

بَلَىٰٓ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرًۭا ﴿١٥﴾

Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.

فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلشَّفَقِ ﴿١٦﴾

To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.

وَٱلَّيْلِ وَمَا وَسَقَ ﴿١٧﴾

Da dare, da abin da ya ƙunsa.

وَٱلْقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ ﴿١٨﴾

Da watã idan (haskensa) ya cika.

لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍۢ ﴿١٩﴾

Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.

فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ ﴿٢٠﴾

To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?

84:21 Ayar sujada

وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ ٱلْقُرْءَانُ لَا يَسْجُدُونَ ۩ ﴿٢١﴾

Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?

بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يُكَذِّبُونَ ﴿٢٢﴾

Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.

وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ ﴿٢٣﴾

Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.

فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ ﴿٢٤﴾

Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍۭ ﴿٢٥﴾

Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.

Al-Inshiqaq Aya 1 cikin 25

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-Inshiqaq

Sura Al-Inshiqaq (الانشقاق) ita ce sura ta 84 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 25 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, الانشقاق, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Inshiqaq

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Inshiqaq?

Sura Al-Inshiqaq tana da ayoyi 25.

Shin Sura Al-Inshiqaq ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Inshiqaq take?

Sura Al-Inshiqaq tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-Inshiqaq?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp