أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ ﴿١﴾
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
Sura ta 107 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ ﴿١﴾
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
فَذَٰلِكَ ٱلَّذِى يَدُعُّ ٱلْيَتِيمَ ﴿٢﴾
To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa).
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ ﴿٣﴾
Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
فَوَيْلٌۭ لِّلْمُصَلِّينَ ﴿٤﴾
To, bone yã tabbata ga masallata.
ٱلَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ ﴿٥﴾
Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.
ٱلَّذِينَ هُمْ يُرَآءُونَ ﴿٦﴾
Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu)
وَيَمْنَعُونَ ٱلْمَاعُونَ ﴿٧﴾
Kuma suna hana taimako.
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura Al-Ma'un (الماعون) ita ce sura ta 107 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 7 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, الماعون, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura Al-Ma'un tana da ayoyi 7.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura Al-Ma'un tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.