Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 82 a Alƙur'ani

Sura Al-Infitar

Makkiyya Aya 19 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتْ ﴿١﴾

Idan sama ta tsãge.

وَإِذَا ٱلْكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتْ ﴿٢﴾

Kuma idan taurãri suka wãtse.

وَإِذَا ٱلْبِحَارُ فُجِّرَتْ ﴿٣﴾

Kuma idan tẽkuna aka facce su.

وَإِذَا ٱلْقُبُورُ بُعْثِرَتْ ﴿٤﴾

Kuma idan kaburbura aka tõne su.

عَلِمَتْ نَفْسٌۭ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ ﴿٥﴾

Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

يَٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلْكَرِيمِ ﴿٦﴾

Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.

ٱلَّذِى خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ ﴿٧﴾

Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

فِىٓ أَىِّ صُورَةٍۢ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ ﴿٨﴾

A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ ﴿٩﴾

A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَٰفِظِينَ ﴿١٠﴾

Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

كِرَامًۭا كَٰتِبِينَ ﴿١١﴾

Mãsu daraja, marubũta.

يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ ﴿١٢﴾

Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍۢ ﴿١٣﴾

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

وَإِنَّ ٱلْفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍۢ ﴿١٤﴾

Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ ٱلدِّينِ ﴿١٥﴾

Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَآئِبِينَ ﴿١٦﴾

Bã zã su faku daga gare ta ba.

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ ﴿١٧﴾

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?

ثُمَّ مَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ ﴿١٨﴾

Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌۭ لِّنَفْسٍۢ شَيْـًۭٔا ۖ وَٱلْأَمْرُ يَوْمَئِذٍۢ لِّلَّهِ ﴿١٩﴾

Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

Al-Infitar Aya 1 cikin 19

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-Infitar

Sura Al-Infitar (الانفطار) ita ce sura ta 82 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 19 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, الانفطار, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Infitar

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Infitar?

Sura Al-Infitar tana da ayoyi 19.

Shin Sura Al-Infitar ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Infitar take?

Sura Al-Infitar tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-Infitar?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp