إِذَا ٱلشَّمْسُ كُوِّرَتْ ﴿١﴾
Idan rãna aka shafe haskenta
Sura ta 81 a Alƙur'ani
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِذَا ٱلشَّمْسُ كُوِّرَتْ ﴿١﴾
Idan rãna aka shafe haskenta
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتْ ﴿٢﴾
Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
وَإِذَا ٱلْجِبَالُ سُيِّرَتْ ﴿٣﴾
Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
وَإِذَا ٱلْعِشَارُ عُطِّلَتْ ﴿٤﴾
Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
وَإِذَا ٱلْوُحُوشُ حُشِرَتْ ﴿٥﴾
Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
وَإِذَا ٱلْبِحَارُ سُجِّرَتْ ﴿٦﴾
Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتْ ﴿٧﴾
Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.
وَإِذَا ٱلْمَوْءُۥدَةُ سُئِلَتْ ﴿٨﴾
Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.
بِأَىِّ ذَنۢبٍۢ قُتِلَتْ ﴿٩﴾
"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتْ ﴿١٠﴾
Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتْ ﴿١١﴾
Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
وَإِذَا ٱلْجَحِيمُ سُعِّرَتْ ﴿١٢﴾
Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
وَإِذَا ٱلْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ ﴿١٣﴾
Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
عَلِمَتْ نَفْسٌۭ مَّآ أَحْضَرَتْ ﴿١٤﴾
Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلْخُنَّسِ ﴿١٥﴾
To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.
ٱلْجَوَارِ ٱلْكُنَّسِ ﴿١٦﴾
Mãsu gudu suna ɓũya.
وَٱلَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ ﴿١٧﴾
Da dare idan ya bãyar da bãya.
وَٱلصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ ﴿١٨﴾
Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍۢ كَرِيمٍۢ ﴿١٩﴾
Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
ذِى قُوَّةٍ عِندَ ذِى ٱلْعَرْشِ مَكِينٍۢ ﴿٢٠﴾
Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
مُّطَاعٍۢ ثَمَّ أَمِينٍۢ ﴿٢١﴾
Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍۢ ﴿٢٢﴾
Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
وَلَقَدْ رَءَاهُ بِٱلْأُفُقِ ٱلْمُبِينِ ﴿٢٣﴾
Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلْغَيْبِ بِضَنِينٍۢ ﴿٢٤﴾
Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَٰنٍۢ رَّجِيمٍۢ ﴿٢٥﴾
Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ ﴿٢٦﴾
Shin, a inã zã ku tafi?
إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌۭ لِّلْعَٰلَمِينَ ﴿٢٧﴾
Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
لِمَن شَآءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ ﴿٢٨﴾
Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَٰلَمِينَ ﴿٢٩﴾
Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.
Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.
Sura At-Takwir (التكوير) ita ce sura ta 81 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 29 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.
Sunanta, التكوير, shi ne yadda ake san surar da Larabci.
Sura At-Takwir tana da ayoyi 29.
Rarrabawa: Makkiyya.
Sura At-Takwir tana Juzu'i na 30.
Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.