Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 96 a Alƙur'ani

Sura Al-'Alaq

Makkiyya Aya 19 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱقْرَأْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلَّذِى خَلَقَ ﴿١﴾

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

خَلَقَ ٱلْإِنسَٰنَ مِنْ عَلَقٍ ﴿٢﴾

Ya hahitta mutum daga gudan jini.

ٱقْرَأْ وَرَبُّكَ ٱلْأَكْرَمُ ﴿٣﴾

Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.

ٱلَّذِى عَلَّمَ بِٱلْقَلَمِ ﴿٤﴾

Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.

عَلَّمَ ٱلْإِنسَٰنَ مَا لَمْ يَعْلَمْ ﴿٥﴾

Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

كَلَّآ إِنَّ ٱلْإِنسَٰنَ لَيَطْغَىٰٓ ﴿٦﴾

A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).

أَن رَّءَاهُ ٱسْتَغْنَىٰٓ ﴿٧﴾

Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.

إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجْعَىٰٓ ﴿٨﴾

Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.

أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يَنْهَىٰ ﴿٩﴾

Shin, kã ga wanda ke hana.

عَبْدًا إِذَا صَلَّىٰٓ ﴿١٠﴾

Bãwã idan yã yi salla?

أَرَءَيْتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلْهُدَىٰٓ ﴿١١﴾

Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?

أَوْ أَمَرَ بِٱلتَّقْوَىٰٓ ﴿١٢﴾

Ko ya yi umurni da taƙawa?

أَرَءَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ ﴿١٣﴾

Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?

أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ ﴿١٤﴾

Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?

كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًۢا بِٱلنَّاصِيَةِ ﴿١٥﴾

A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.

نَاصِيَةٍۢ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٍۢ ﴿١٦﴾

Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.

فَلْيَدْعُ نَادِيَهُۥ ﴿١٧﴾

Sai ya kirayi ƙungiyarsa.

سَنَدْعُ ٱلزَّبَانِيَةَ ﴿١٨﴾

Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).

96:19 Ayar sujada

كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَٱسْجُدْ وَٱقْتَرِب ۩ ﴿١٩﴾

A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).

Al-'Alaq Aya 1 cikin 19

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-'Alaq

Sura Al-'Alaq (العلق) ita ce sura ta 96 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 19 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, العلق, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-'Alaq

Ayoyi nawa ne a Sura Al-'Alaq?

Sura Al-'Alaq tana da ayoyi 19.

Shin Sura Al-'Alaq ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-'Alaq take?

Sura Al-'Alaq tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-'Alaq?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp