Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 79 a Alƙur'ani

Sura An-Nazi'at

Makkiyya Aya 46 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلنَّٰزِعَٰتِ غَرْقًۭا ﴿١﴾

Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.

وَٱلنَّٰشِطَٰتِ نَشْطًۭا ﴿٢﴾

Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.

وَٱلسَّٰبِحَٰتِ سَبْحًۭا ﴿٣﴾

Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

فَٱلسَّٰبِقَٰتِ سَبْقًۭا ﴿٤﴾

Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.

فَٱلْمُدَبِّرَٰتِ أَمْرًۭا ﴿٥﴾

Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.

يَوْمَ تَرْجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ ﴿٦﴾

Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.

تَتْبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ ﴿٧﴾

Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.

قُلُوبٌۭ يَوْمَئِذٍۢ وَاجِفَةٌ ﴿٨﴾

Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.

أَبْصَٰرُهَا خَٰشِعَةٌۭ ﴿٩﴾

Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.

يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِى ٱلْحَافِرَةِ ﴿١٠﴾

Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?

أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمًۭا نَّخِرَةًۭ ﴿١١﴾

"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"

قَالُوا۟ تِلْكَ إِذًۭا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌۭ ﴿١٢﴾

Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"

فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌۭ وَٰحِدَةٌۭ ﴿١٣﴾

To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.

فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ ﴿١٤﴾

Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.

هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ ﴿١٥﴾

Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?

إِذْ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلْوَادِ ٱلْمُقَدَّسِ طُوًى ﴿١٦﴾

A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?

ٱذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ ﴿١٧﴾

Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.

فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ ﴿١٨﴾

"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.

وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ ﴿١٩﴾

"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"

فَأَرَىٰهُ ٱلْءَايَةَ ٱلْكُبْرَىٰ ﴿٢٠﴾

Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.

فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ ﴿٢١﴾

Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),

ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ ﴿٢٢﴾

Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.

فَحَشَرَ فَنَادَىٰ ﴿٢٣﴾

Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.

فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلْأَعْلَىٰ ﴿٢٤﴾

Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."

فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلْءَاخِرَةِ وَٱلْأُولَىٰٓ ﴿٢٥﴾

Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَعِبْرَةًۭ لِّمَن يَخْشَىٰٓ ﴿٢٦﴾

Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.

ءَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُ ۚ بَنَىٰهَا ﴿٢٧﴾

Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.

رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّىٰهَا ﴿٢٨﴾

Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.

وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَىٰهَا ﴿٢٩﴾

Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.

وَٱلْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ ﴿٣٠﴾

Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.

أَخْرَجَ مِنْهَا مَآءَهَا وَمَرْعَىٰهَا ﴿٣١﴾

Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.

وَٱلْجِبَالَ أَرْسَىٰهَا ﴿٣٢﴾

Da duwatsu, Yã kafe ta.

مَتَٰعًۭا لَّكُمْ وَلِأَنْعَٰمِكُمْ ﴿٣٣﴾

Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلْكُبْرَىٰ ﴿٣٤﴾

To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.

يَوْمَ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَٰنُ مَا سَعَىٰ ﴿٣٥﴾

Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.

وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ ﴿٣٦﴾

Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.

فَأَمَّا مَن طَغَىٰ ﴿٣٧﴾

To, amma wanda ya yi girman kai.

وَءَاثَرَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا ﴿٣٨﴾

Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).

فَإِنَّ ٱلْجَحِيمَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ ﴿٣٩﴾

To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.

وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفْسَ عَنِ ٱلْهَوَىٰ ﴿٤٠﴾

Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.

فَإِنَّ ٱلْجَنَّةَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ ﴿٤١﴾

To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.

يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَىٰهَا ﴿٤٢﴾

Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?

فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَىٰهَآ ﴿٤٣﴾

Me ya haɗã ka da ambatonta?

إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ ﴿٤٤﴾

Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.

إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَىٰهَا ﴿٤٥﴾

Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.

كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوٓا۟ إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَىٰهَا ﴿٤٦﴾

Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.

An-Nazi'at Aya 1 cikin 46

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura An-Nazi'at

Sura An-Nazi'at (النازعات) ita ce sura ta 79 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 46 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, النازعات, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura An-Nazi'at

Ayoyi nawa ne a Sura An-Nazi'at?

Sura An-Nazi'at tana da ayoyi 46.

Shin Sura An-Nazi'at ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura An-Nazi'at take?

Sura An-Nazi'at tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura An-Nazi'at?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp