Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 75 a Alƙur'ani

Sura Al-Qiyamah

Makkiyya Aya 40 Juzu'i 29

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

لَآ أُقْسِمُ بِيَوْمِ ٱلْقِيَٰمَةِ ﴿١﴾

Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.

وَلَآ أُقْسِمُ بِٱلنَّفْسِ ٱللَّوَّامَةِ ﴿٢﴾

Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.

أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُۥ ﴿٣﴾

Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?

بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّىَ بَنَانَهُۥ ﴿٤﴾

Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.

بَلْ يُرِيدُ ٱلْإِنسَٰنُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُۥ ﴿٥﴾

Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.

يَسْـَٔلُ أَيَّانَ يَوْمُ ٱلْقِيَٰمَةِ ﴿٦﴾

Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"

فَإِذَا بَرِقَ ٱلْبَصَرُ ﴿٧﴾

To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

وَخَسَفَ ٱلْقَمَرُ ﴿٨﴾

Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

وَجُمِعَ ٱلشَّمْسُ وَٱلْقَمَرُ ﴿٩﴾

Aka tãra rãnã da watã

يَقُولُ ٱلْإِنسَٰنُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ ٱلْمَفَرُّ ﴿١٠﴾

Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"

كَلَّا لَا وَزَرَ ﴿١١﴾

A'aha! bãbu mafaka.

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ ٱلْمُسْتَقَرُّ ﴿١٢﴾

zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

يُنَبَّؤُا۟ ٱلْإِنسَٰنُ يَوْمَئِذٍۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ ﴿١٣﴾

Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

بَلِ ٱلْإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفْسِهِۦ بَصِيرَةٌۭ ﴿١٤﴾

Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.

وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ ﴿١٥﴾

Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).

لَا تُحَرِّكْ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِۦٓ ﴿١٦﴾

Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).

إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُۥ وَقُرْءَانَهُۥ ﴿١٧﴾

Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.

فَإِذَا قَرَأْنَٰهُ فَٱتَّبِعْ قُرْءَانَهُۥ ﴿١٨﴾

To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.

ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُۥ ﴿١٩﴾

sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.

كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ ٱلْعَاجِلَةَ ﴿٢٠﴾

A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.

وَتَذَرُونَ ٱلْءَاخِرَةَ ﴿٢١﴾

Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).

وُجُوهٌۭ يَوْمَئِذٍۢ نَّاضِرَةٌ ﴿٢٢﴾

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.

إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌۭ ﴿٢٣﴾

Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.

وَوُجُوهٌۭ يَوْمَئِذٍۭ بَاسِرَةٌۭ ﴿٢٤﴾

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.

تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌۭ ﴿٢٥﴾

Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.

كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِىَ ﴿٢٦﴾

A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.

وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍۢ ﴿٢٧﴾

kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"

وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلْفِرَاقُ ﴿٢٨﴾

Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.

وَٱلْتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ ﴿٢٩﴾

Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ ٱلْمَسَاقُ ﴿٣٠﴾

Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.

فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ ﴿٣١﴾

To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!

وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ﴿٣٢﴾

Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!

ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ ﴿٣٣﴾

Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.

أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ ﴿٣٤﴾

Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.

ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰٓ ﴿٣٥﴾

Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.

أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَٰنُ أَن يُتْرَكَ سُدًى ﴿٣٦﴾

Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?

أَلَمْ يَكُ نُطْفَةًۭ مِّن مَّنِىٍّۢ يُمْنَىٰ ﴿٣٧﴾

Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)

ثُمَّ كَانَ عَلَقَةًۭ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ ﴿٣٨﴾

Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;

فَجَعَلَ مِنْهُ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ ﴿٣٩﴾

Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?

أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحْۦِىَ ٱلْمَوْتَىٰ ﴿٤٠﴾

Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?

Al-Qiyamah Aya 1 cikin 40

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-Qiyamah

Sura Al-Qiyamah (القيامة) ita ce sura ta 75 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 40 kuma tana cikin Juzu'i na 29. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, القيامة, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Qiyamah

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Qiyamah?

Sura Al-Qiyamah tana da ayoyi 40.

Shin Sura Al-Qiyamah ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Qiyamah take?

Sura Al-Qiyamah tana Juzu'i na 29.

A ina zan saurari Sura Al-Qiyamah?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

WhatsApp