Ana gwada Muslim Flow, kuma za ta zo Google Play nan ba da daɗewa ba. Zazzagewa

Sura ta 98 a Alƙur'ani

Sura Al-Bayyinah

Madaniyya Aya 8 Juzu'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

لَمْ يَكُنِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَٰبِ وَٱلْمُشْرِكِينَ مُنفَكِّينَ حَتَّىٰ تَأْتِيَهُمُ ٱلْبَيِّنَةُ ﴿١﴾

Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu.

رَسُولٌۭ مِّنَ ٱللَّهِ يَتْلُوا۟ صُحُفًۭا مُّطَهَّرَةًۭ ﴿٢﴾

Wani Manzo daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki.

فِيهَا كُتُبٌۭ قَيِّمَةٌۭ ﴿٣﴾

A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja.

وَمَا تَفَرَّقَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَٰبَ إِلَّا مِنۢ بَعْدِ مَا جَآءَتْهُمُ ٱلْبَيِّنَةُ ﴿٤﴾

Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu.

وَمَآ أُمِرُوٓا۟ إِلَّا لِيَعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤْتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ ۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلْقَيِّمَةِ ﴿٥﴾

Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai.

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَٰبِ وَٱلْمُشْرِكِينَ فِى نَارِ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ ۚ أُو۟لَٰٓئِكَ هُمْ شَرُّ ٱلْبَرِيَّةِ ﴿٦﴾

Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai.

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أُو۟لَٰٓئِكَ هُمْ خَيْرُ ٱلْبَرِيَّةِ ﴿٧﴾

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta.

جَزَآؤُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّٰتُ عَدْنٍۢ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًۭا ۖ رَّضِىَ ٱللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا۟ عَنْهُ ۚ ذَٰلِكَ لِمَنْ خَشِىَ رَبَّهُۥ ﴿٨﴾

Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa.

Al-Bayyinah Aya 1 cikin 8

Rubutun Larabci: rubutun Usmani. Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi. Sauti: everyayah.com.

Game da Sura Al-Bayyinah

Sura Al-Bayyinah (البينة) ita ce sura ta 98 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 8 kuma tana cikin Juzu'i na 30. An ware ta a matsayin sura ta Madaniyya, wato an saukar da ita galibi bayan hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, البينة, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Bayyinah

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Bayyinah?

Sura Al-Bayyinah tana da ayoyi 8.

Shin Sura Al-Bayyinah ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Madaniyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Bayyinah take?

Sura Al-Bayyinah tana Juzu'i na 30.

A ina zan saurari Sura Al-Bayyinah?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Abdur-Rahman As-Sudais, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Mohamed Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.