Sura ta 77 a Alƙur'ani

Sura Al-Mursalat

MakkiyyaAya 50Juzu'i 29
Al-Mursalat

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلْمُرْسَلَٰتِ عُرْفًۭا ﴿١﴾

Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَٱلْعَٰصِفَٰتِ عَصْفًۭا ﴿٢﴾

Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشْرًۭا ﴿٣﴾

Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَٱلْفَٰرِقَٰتِ فَرْقًۭا ﴿٤﴾

sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَٱلْمُلْقِيَٰتِ ذِكْرًا ﴿٥﴾

Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

عُذْرًا أَوْ نُذْرًا ﴿٦﴾

Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٌۭ ﴿٧﴾

Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتْ ﴿٨﴾

To, idan taurãri aka shãfe haskensu.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتْ ﴿٩﴾

Kuma, idan sama aka tsãge ta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا ٱلْجِبَالُ نُسِفَتْ ﴿١٠﴾

Kuma, idan duwãtsu aka nike su.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتْ ﴿١١﴾

Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

لِأَىِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ ﴿١٢﴾

Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

لِيَوْمِ ٱلْفَصْلِ ﴿١٣﴾

Domin rãnar rarrabẽwa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ ﴿١٤﴾

Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿١٥﴾

Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

أَلَمْ نُهْلِكِ ٱلْأَوَّلِينَ ﴿١٦﴾

Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ ٱلْءَاخِرِينَ ﴿١٧﴾

Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِٱلْمُجْرِمِينَ ﴿١٨﴾

Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿١٩﴾

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّآءٍۢ مَّهِينٍۢ ﴿٢٠﴾

Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَجَعَلْنَٰهُ فِى قَرَارٍۢ مَّكِينٍ ﴿٢١﴾

Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِلَىٰ قَدَرٍۢ مَّعْلُومٍۢ ﴿٢٢﴾

Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ ٱلْقَٰدِرُونَ ﴿٢٣﴾

Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٢٤﴾

Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ كِفَاتًا ﴿٢٥﴾

Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

أَحْيَآءًۭ وَأَمْوَٰتًۭا ﴿٢٦﴾

Ga rãyayyu da matattu,

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ شَٰمِخَٰتٍۢ وَأَسْقَيْنَٰكُم مَّآءًۭ فُرَاتًۭا ﴿٢٧﴾

Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٢٨﴾

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ﴿٢٩﴾

Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ ظِلٍّۢ ذِى ثَلَٰثِ شُعَبٍۢ ﴿٣٠﴾

Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

لَّا ظَلِيلٍۢ وَلَا يُغْنِى مِنَ ٱللَّهَبِ ﴿٣١﴾

Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِنَّهَا تَرْمِى بِشَرَرٍۢ كَٱلْقَصْرِ ﴿٣٢﴾

Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٌۭ صُفْرٌۭ ﴿٣٣﴾

Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٣٤﴾

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

هَٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ ﴿٣٥﴾

Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ ﴿٣٦﴾

Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٣٧﴾

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

هَٰذَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَٰكُمْ وَٱلْأَوَّلِينَ ﴿٣٨﴾

Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌۭ فَكِيدُونِ ﴿٣٩﴾

To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٤٠﴾

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى ظِلَٰلٍۢ وَعُيُونٍۢ ﴿٤١﴾

Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ ﴿٤٢﴾

Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ ﴿٤٣﴾

(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ ﴿٤٤﴾

Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٤٥﴾

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

كُلُوا۟ وَتَمَتَّعُوا۟ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ ﴿٤٦﴾

(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٤٧﴾

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرْكَعُوا۟ لَا يَرْكَعُونَ ﴿٤٨﴾

Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

وَيْلٌۭ يَوْمَئِذٍۢ لِّلْمُكَذِّبِينَ ﴿٤٩﴾

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

فَبِأَىِّ حَدِيثٍۭ بَعْدَهُۥ يُؤْمِنُونَ ﴿٥٠﴾

To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni

Tafsirin al-Muyassar (Larabci)

Al-MursalatAya 1 cikin 50

Game da Sura Al-Mursalat

Sura Al-Mursalat (المرسلات) ita ce sura ta 77 a Alƙur'ani. Tana da ayoyi 50 kuma tana cikin Juzu'i na 29. An ware ta a matsayin sura ta Makkiyya, wato an saukar da ita galibi kafin hijirar Annabi zuwa Madina.

Sunanta, المرسلات, shi ne yadda ake san surar da Larabci.

Tambayoyi game da Sura Al-Mursalat

Ayoyi nawa ne a Sura Al-Mursalat?

Sura Al-Mursalat tana da ayoyi 50.

Shin Sura Al-Mursalat ta Makkiyya ce ko ta Madaniyya?

Rarrabawa: Makkiyya.

A wane Juzu'i Sura Al-Mursalat take?

Sura Al-Mursalat tana Juzu'i na 29.

A ina zan saurari Sura Al-Mursalat?

Danna Kunna a wannan shafin don jin ta aya bayan aya, Abdur-Rahman As-Sudais, Mishary Alafasy, Mahmoud Khalil Al-Husary, Abdul Basit Abdus-Samad, Maher Al-Muaiqly, Saad Al-Ghamdi, Ahmad Al-Ajmi, Abu Bakr Ash-Shatri, Hani Ar-Rifai, Muhammad Siddiq Al-Minshawi, Ali Al-Hudhaify, Muhammad Ayyub, Abdullah Basfar, Yasser Ad-Dosari, Nasser Al-Qatami, Salah Al-Budair, Saud Ash-Shuraim, Abdullah Awad Al-Juhany, Muhammad Jibreel ne ke karantawa.

Samu manhajar

Samu aGoogle Play

This page is translated with machine assistance and may contain mistakes. The English and Arabic versions are our reference. About our sources