۞ قَالَ ٱلْمَلَأُ ٱلَّذِينَ ٱسْتَكْبَرُوا۟ مِن قَوْمِهِۦ لَنُخْرِجَنَّكَ يَٰشُعَيْبُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَعَكَ مِن قَرْيَتِنَآ أَوْ لَتَعُودُنَّ فِى مِلَّتِنَا ۚ قَالَ أَوَلَوْ كُنَّا كَٰرِهِينَ ﴿٨٨﴾
Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?"
قَدِ ٱفْتَرَيْنَا عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا إِنْ عُدْنَا فِى مِلَّتِكُم بَعْدَ إِذْ نَجَّىٰنَا ٱللَّهُ مِنْهَا ۚ وَمَا يَكُونُ لَنَآ أَن نَّعُودَ فِيهَآ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّنَا ۚ وَسِعَ رَبُّنَا كُلَّ شَىْءٍ عِلْمًا ۚ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلْنَا ۚ رَبَّنَا ٱفْتَحْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ قَوْمِنَا بِٱلْحَقِّ وَأَنتَ خَيْرُ ٱلْفَٰتِحِينَ ﴿٨٩﴾
"Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci."
وَقَالَ ٱلْمَلَأُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن قَوْمِهِۦ لَئِنِ ٱتَّبَعْتُمْ شُعَيْبًا إِنَّكُمْ إِذًۭا لَّخَٰسِرُونَ ﴿٩٠﴾
Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne."
فَأَخَذَتْهُمُ ٱلرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا۟ فِى دَارِهِمْ جَٰثِمِينَ ﴿٩١﴾
Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne.
ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ شُعَيْبًۭا كَأَن لَّمْ يَغْنَوْا۟ فِيهَا ۚ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ شُعَيْبًۭا كَانُوا۟ هُمُ ٱلْخَٰسِرِينَ ﴿٩٢﴾
Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra!
فَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَٰقَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَٰلَٰتِ رَبِّى وَنَصَحْتُ لَكُمْ ۖ فَكَيْفَ ءَاسَىٰ عَلَىٰ قَوْمٍۢ كَٰفِرِينَ ﴿٩٣﴾
Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?"
وَلَمَّا جَآءَ أَمْرُنَا نَجَّيْنَا شُعَيْبًۭا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَعَهُۥ بِرَحْمَةٍۢ مِّنَّا وَأَخَذَتِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ٱلصَّيْحَةُ فَأَصْبَحُوا۟ فِى دِيَٰرِهِمْ جَٰثِمِينَ ﴿٩٤﴾
Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama waɗanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu.
كَأَن لَّمْ يَغْنَوْا۟ فِيهَآ ۗ أَلَا بُعْدًۭا لِّمَدْيَنَ كَمَا بَعِدَتْ ثَمُودُ ﴿٩٥﴾
Kamar ba su zaunã ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda Samũdãwa suka halaka.